This blog was created by Comrade Jibril Almustapha Gusau. The blog will provide you with sound, authentic and genuine news across the world
Monday, 10 July 2017
Nazari: MAKOMAR DAN TALAKA A JIHAR ZAMFARA.
Daga: Ahmad Ibrahim Dan Wudil
Matashiya:
Shin Ko Kasan Cewa Akwai Matasa 'Ya'yan Talakawa Bila Adadin Da Suka Gama Makarantar Gaba Da Sakandire Kuma Basa Da Aikinyi?
Babu Daya Daga Cikin 'Ya'yan Gwamna Ko Mataimakin Gwamna Ko Wani Mai Riqe Da Madafun Iko Wanda Dan Sa Ya Gama Makarantar Gaba Da Sakandire Kuma Yake Zaune Babu Aiki. Wai Mai Yasa Haka?
Dayawa Daga Cikin 'Ya'yan Masu Riqe Da Madafun Iko Suna Aiki Ne A Matakai Masu Karfi. Shin Mene Ne Yasa Muma 'Yay'an Talaka Ba Za'a Nema Mana Ayyukanyi Ba?
Da Farko Dai Sanin Kowane Cewa Jahar Zamfara Jaha Ce Ta Masu Ilimi Da Hankali. Hakan Ne Ma Yasa Da Zarar An Kira Ka Da Dan Zamfara Sai Kaga Mutane Nayi Maka Kallon Mai Ilimi Hankali Da Sanin Ya Kamata
Sai Dai Tun A Lokacin Da Jahar Zamfara Ta Samu Jaha Akayi Rashin Sa'a Da Gwamnoni Wadanda Tabbas Ba Cigaban Al'ummar Jihar Zamfara Ne A Zuciyar Su Ba Sunyi Mana Illah Fiye Da Tunanin Mai Tunani.
Idan Ma Zamu Iya Tunawa A Wadannan Shekaru Biyu Da Suka Shige Ne Jahar Zamfara Take Fuskantar Wani Babban Kalubale Na Tsaikon Biyama Yara 'Yan Ajin Karshe Kudin Jarabawa Da Gwamnati Tayi Wanda Hakan Ne Ma Yasa Da Yawan Yara Suka Samu Tsaikon Zuwa Makaranta.
Abun Takaici Kuma Shine Tun Kafuwar Wannan Gwamnati Ta Addinin Mu Al'ummar Mu Har Yanzu Taki Ta Dauki Ma'aikaci Ko Daya A Jihar Zamfara Kuma Al'umma Suna Gani Sunki Yin Magana Akan Wannan Illar
Na Tabbata Nan Gaba Zamu Gane Hakan Don Babban Tabo Ne Wanda Bazai Iya Goguwa Ba.
Ina Makomar 'Ya'yan Talakawan Da Basa Zuwa Makaranta Ayau ? Gobe Fa Su Ne Zasu Iya Zama 'Yan Tasha, 'Yan Shaye-Shaye, Marasa Gata Da Aikinyi.
A Gefe Daya Kuma Zanso Kayi Duba Yakai Mai Karatu Izuwa Ga Wani Abun Tausayi.
Dan Talaka Ne Ya Saida Akuya, Tunkiya, Fegi, Da Dukkannin Wani Abu Nasa Domin Ya Samu Ilimin Zamani. Kuma Wai Sai Aka Wayi Gari Ya Gama Wannan Karatun Din Kuma Babu Aikin Yi. Wannan Abun Tausayi Har Ina! Yi Duba Da Idon Basira Wannan Jihar Tamu Tuni Dan Talakka Ma Ya Fara Yanke Kauna Ga Samun Sauki A Kusa, Saboda Abubuwan Da Ya Gani A Kasa Na Nuna Banbanci A Tsantsagoran Gaskiya.
YI TUNANI MAI KYAU. INA MAFITA GA DAN TALAKKA ?
Sunday, 9 July 2017
YADDA AKE YIWA DAN MAJALISA KIRANYE
Daga: Kwamared Jibril Almustapha Gusau
Kiranye: Na nufin dawo da halastaccen zababben dan majalisar dattijai ko majalisar wakilai zuwa gida. Ana yin zaben raba gardama ne (na EH ko A'A) ta haka ne za'a gano yawan masu son ya dawo da kuma masu son ya cigaba da zama a zauren majalisa.
Kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 (wanda aka yiwa gyaran fuska) ya halasta yin kiranye, a Sashe na 69 mai taken KIRANYE
Saboda haka, kiranye ya halasta a Najeriya !
HANYOYI UKU DA AKE BI WAJEN YIN KIRANYE
(1) RUBUTA TUHUMA DA KORAFI: Za'a iya dawo da dan majalisar dattijai da kuma majalisar wakilai zuwa gida ta hanyar rubuta korafi zuwa ga Shugaban Hukumar Zabe ta kasa mai cin gashin kan ta wato INEC. A madadin daukacin al'ummar wannan mazaba, wadanda zasu rattaba hannu akan korafin. Ana bukatar masu son dan majalisar ya dawo gida su fi rinjaye. Misali, idan a wannan mazabar akwai halastattun masu jefa kuri'a mutum 1000, to ana bukatar mutum 501 su rattaba hannu akan wannan takarda ta tuhuma.
(2) TANTANCE SA HANNUN AL'UMMAR MAZABA
Bayan hukumar zabe ta INEC ta karbi wadannan takardu, to zata sanar da dan majalisar halin da ake ciki. Daga nan, sai hukumar ta saka ranar tantance halascin sa hannun al'ummar wannan mazaba masu son dan majalisar ya dawo gida. Ta hanyar dauko kundin rijistar masu jefa kuri'a da hukumar INEC ta tanadar.
3- ZABEN RABA GARDAMA
Idan har aka tsallake wannan matakai biyu da suka gabata, sai hukumar zabe ta INEC ta shirya zaben raba gardama. A nan, za'a nemi al'ummar wannan mazabar su jefa kuri'ar amincewa ko kin amincewa da zaman dan majalisar. Kuma za'a yi wannan zabe ne cikin kwanaki 90.
Idan har masu son da majalisar ya dawo suka fi rinjaye, to hukumar zabe ta kasa (INEC) zata rubuta takardar umarni zuwa ga Shugaban Majaisar dattijai (idan sanata ne ake so ya dawo) ko kuma Shugaban Majalisar wakilai (Idan wakili ne ake so ya dawo), inda hukumae INEC zata umarce su da su gaggauta koro wannan dan majalisar har sai al'ummar yankin sun zabi sabon Sanata ko kuma wakili.
Wadannan sune matakan yin kiranyen da majalisa a Naeriya.
Comrade Jibril Amustapha Gusau,
Human Rights Activist.
Ba Mu Gamsu Da Wakilin Gusau Da Tsafe Ba
Ba Mu Gamsu Da Wakilin Gusau Da Tsafe Ba-Inji Kwamared Jibril Almustapha.
Daga Lawal Wali Tsafe
Wani matashi dan gwagwarmayar kare hakkin dan-Adam Kwamared Jibril Almustapha Gusau ya bayyana cewa, matasan yankin Gusau da Tsafe dabke jihar Zamfara ba su gamsu da wakilcin wakilin su a majalisar wakilai ba.
A zantawarsa da wakilin Zuma Times Hausa, ya bayyana cewa: "Sama da shekaru biyu kenan da al'ummar wannan yanki suka tura Honarabul Isah Ibrahim Ruwan Doruwa a majalisar wakilai, amma kawo yanzu babu wani aikin azo a gani da yayi a yakin.
"Haka ma babu wani katamammen kudiri da wakilin ya gabatar a majalisar. A takaice, al'ummomin Gusau da Tsafe ba su san dadin wakilcin wannan wakili nasu ba."
Ya kara da cewa: "Za mu hada hannu da kungiyoyin sa-kai na matasa domin mu yi duk mai yiyuwa don ganin mun jawo hankalin wakilin. Idan kuma bai juyo kan yi wa talakawan wannan yanki ayyukan more rayuwa ba, to zamu iya daukar matakin yi masa kiranye kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
©Zuma Times Hausa.
Friday, 7 July 2017
Gusau/Tsafe Lose Confidence in their Rep.
GUSAU/TSAFE ELECTORATES LOSE CONFIDENCE IN THEIR REPRESENTATIVE
It is quite clear to every inhabitant of Gusau/Tsafe Local Government Areas that, their representative sent to the Green chamber brings nothing but backwardness to the constituency for 2 consecutive years of his representation.
It was indicated that, he neither rise a motion nor proposals. In a nutshell, he has nothing important in him.
I have been watching National Assembly plenaries for a long, but I have never spotted the bench warmer speaking in the chamber.
What always comes to my mind is that, what's preventing him from performing well in the National Assembly? But, I later soundly discovered that, the major mistake was made by the electorates who sent an uncivilized, irresponsible, incapable, unenergized, inerudite, benighted, lowbrow and untutored personality to represent them in the lower chamber.
I am pretty sure that, a Head boy of a secondary school can perform more better than this imbecile and nincompoop individual.
What an opprobrium !
We must break our silence !
We must speak loudly !
We are not voiceless !
Matasan Zamfara Ta Tsakiya Ta Aminta Da Sanata Marafa A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jiha...
Kungiyar Hadakar Matasan Zamfara Ta Tsakiya ta bayyana goyon bayanta ga tsayawa takarar neman kujerar gwamnan jihar Zamfara da Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya yake kudurin yi a babban zaben gama gari na shekarar 2019 mai zuwa.
Shugaban kungiyar, Rufa'i Bala UB ne ya bayyana hakan a lokacin wata ziyarar ban-girma ta barka da sallah da kungiyar ta kai wa Sanata Kabiru Garba Marafa a gidan sa dake garin 'Yandoton Daji dake karamar hukumar mulki ta Tsafe.
Bala UB ya bayyana cewa: "Duba da kulawar da Sanatan yake ba al'ummar yankin sa, kungiyarsa ta aminta da cewa, Sanata Kabiru Garba Marafa ne dan takarar da yafi kowa cancantar ya nemi kujerar gwamnan jihar a babban zabe mai zuwa."
Da yake mayar da jawabi a lokacin ziyarar, Sanata Kabiru Garba Marafa yayi wa Kungiyar Hadakar Matasan Zamfara Ta Tsakiya alkawarin babur mai kafa uku (Keke-Napep) har guda Arba'in da Shida (46) da kuma yiwa kungiyar alkawarin samar mata da ofisodhin gudanarwa a dukkan gundumomi Arba'in da uku dake yankin.
Subscribe to:
Posts (Atom)





