Monday, 10 July 2017

Nazari: MAKOMAR DAN TALAKA A JIHAR ZAMFARA.



Daga: Ahmad Ibrahim Dan Wudil


Matashiya:
Shin Ko Kasan Cewa Akwai Matasa 'Ya'yan Talakawa Bila Adadin Da Suka Gama Makarantar Gaba Da Sakandire Kuma Basa Da Aikinyi?

 Babu Daya Daga Cikin 'Ya'yan Gwamna Ko Mataimakin Gwamna Ko Wani Mai Riqe Da Madafun Iko Wanda Dan Sa Ya Gama Makarantar Gaba Da Sakandire Kuma Yake Zaune Babu Aiki.  Wai Mai Yasa Haka?

Dayawa Daga Cikin 'Ya'yan Masu Riqe Da Madafun Iko Suna Aiki Ne A Matakai Masu Karfi. Shin  Mene Ne Yasa Muma 'Yay'an Talaka Ba Za'a Nema Mana Ayyukanyi Ba?

Da Farko Dai Sanin Kowane Cewa Jahar Zamfara  Jaha Ce Ta Masu  Ilimi Da Hankali. Hakan Ne Ma Yasa Da Zarar An Kira Ka Da Dan Zamfara  Sai Kaga Mutane Nayi Maka Kallon Mai Ilimi Hankali Da Sanin Ya Kamata

 Sai Dai Tun A Lokacin Da Jahar Zamfara  Ta Samu Jaha  Akayi Rashin  Sa'a Da Gwamnoni Wadanda Tabbas Ba Cigaban Al'ummar Jihar Zamfara Ne A Zuciyar Su Ba Sunyi Mana Illah Fiye Da Tunanin Mai Tunani.

Idan Ma Zamu Iya Tunawa A Wadannan Shekaru Biyu Da Suka Shige Ne Jahar Zamfara  Take Fuskantar Wani Babban Kalubale Na Tsaikon  Biyama Yara 'Yan Ajin Karshe Kudin Jarabawa Da Gwamnati  Tayi Wanda Hakan Ne Ma Yasa Da Yawan Yara Suka Samu  Tsaikon Zuwa Makaranta.

Abun Takaici Kuma Shine Tun Kafuwar Wannan Gwamnati Ta Addinin Mu Al'ummar Mu  Har Yanzu Taki Ta Dauki Ma'aikaci Ko Daya A Jihar Zamfara Kuma Al'umma Suna Gani Sunki Yin Magana Akan Wannan  Illar

Na Tabbata Nan Gaba Zamu Gane Hakan Don Babban Tabo Ne Wanda Bazai Iya Goguwa Ba.

Ina Makomar 'Ya'yan Talakawan Da Basa Zuwa Makaranta Ayau ? Gobe Fa Su Ne Zasu Iya Zama 'Yan Tasha, 'Yan Shaye-Shaye, Marasa Gata Da Aikinyi.

A Gefe Daya Kuma Zanso Kayi Duba Yakai Mai Karatu Izuwa Ga Wani Abun Tausayi.

 Dan Talaka Ne Ya Saida Akuya, Tunkiya, Fegi, Da Dukkannin Wani Abu Nasa Domin Ya Samu Ilimin Zamani. Kuma Wai Sai Aka Wayi Gari  Ya Gama Wannan Karatun  Din Kuma Babu Aikin Yi. Wannan Abun Tausayi Har Ina! Yi Duba Da Idon Basira Wannan Jihar Tamu Tuni Dan Talakka Ma Ya Fara Yanke Kauna Ga Samun Sauki A Kusa, Saboda Abubuwan Da Ya Gani A Kasa Na Nuna Banbanci A Tsantsagoran Gaskiya.

YI TUNANI MAI KYAU. INA MAFITA GA DAN TALAKKA ?

No comments: