This blog was created by Comrade Jibril Almustapha Gusau. The blog will provide you with sound, authentic and genuine news across the world
Sunday, 9 July 2017
YADDA AKE YIWA DAN MAJALISA KIRANYE
Daga: Kwamared Jibril Almustapha Gusau
Kiranye: Na nufin dawo da halastaccen zababben dan majalisar dattijai ko majalisar wakilai zuwa gida. Ana yin zaben raba gardama ne (na EH ko A'A) ta haka ne za'a gano yawan masu son ya dawo da kuma masu son ya cigaba da zama a zauren majalisa.
Kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999 (wanda aka yiwa gyaran fuska) ya halasta yin kiranye, a Sashe na 69 mai taken KIRANYE
Saboda haka, kiranye ya halasta a Najeriya !
HANYOYI UKU DA AKE BI WAJEN YIN KIRANYE
(1) RUBUTA TUHUMA DA KORAFI: Za'a iya dawo da dan majalisar dattijai da kuma majalisar wakilai zuwa gida ta hanyar rubuta korafi zuwa ga Shugaban Hukumar Zabe ta kasa mai cin gashin kan ta wato INEC. A madadin daukacin al'ummar wannan mazaba, wadanda zasu rattaba hannu akan korafin. Ana bukatar masu son dan majalisar ya dawo gida su fi rinjaye. Misali, idan a wannan mazabar akwai halastattun masu jefa kuri'a mutum 1000, to ana bukatar mutum 501 su rattaba hannu akan wannan takarda ta tuhuma.
(2) TANTANCE SA HANNUN AL'UMMAR MAZABA
Bayan hukumar zabe ta INEC ta karbi wadannan takardu, to zata sanar da dan majalisar halin da ake ciki. Daga nan, sai hukumar ta saka ranar tantance halascin sa hannun al'ummar wannan mazaba masu son dan majalisar ya dawo gida. Ta hanyar dauko kundin rijistar masu jefa kuri'a da hukumar INEC ta tanadar.
3- ZABEN RABA GARDAMA
Idan har aka tsallake wannan matakai biyu da suka gabata, sai hukumar zabe ta INEC ta shirya zaben raba gardama. A nan, za'a nemi al'ummar wannan mazabar su jefa kuri'ar amincewa ko kin amincewa da zaman dan majalisar. Kuma za'a yi wannan zabe ne cikin kwanaki 90.
Idan har masu son da majalisar ya dawo suka fi rinjaye, to hukumar zabe ta kasa (INEC) zata rubuta takardar umarni zuwa ga Shugaban Majaisar dattijai (idan sanata ne ake so ya dawo) ko kuma Shugaban Majalisar wakilai (Idan wakili ne ake so ya dawo), inda hukumae INEC zata umarce su da su gaggauta koro wannan dan majalisar har sai al'ummar yankin sun zabi sabon Sanata ko kuma wakili.
Wadannan sune matakan yin kiranyen da majalisa a Naeriya.
Comrade Jibril Amustapha Gusau,
Human Rights Activist.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment