This blog was created by Comrade Jibril Almustapha Gusau. The blog will provide you with sound, authentic and genuine news across the world
Sunday, 9 July 2017
Ba Mu Gamsu Da Wakilin Gusau Da Tsafe Ba
Ba Mu Gamsu Da Wakilin Gusau Da Tsafe Ba-Inji Kwamared Jibril Almustapha.
Daga Lawal Wali Tsafe
Wani matashi dan gwagwarmayar kare hakkin dan-Adam Kwamared Jibril Almustapha Gusau ya bayyana cewa, matasan yankin Gusau da Tsafe dabke jihar Zamfara ba su gamsu da wakilcin wakilin su a majalisar wakilai ba.
A zantawarsa da wakilin Zuma Times Hausa, ya bayyana cewa: "Sama da shekaru biyu kenan da al'ummar wannan yanki suka tura Honarabul Isah Ibrahim Ruwan Doruwa a majalisar wakilai, amma kawo yanzu babu wani aikin azo a gani da yayi a yakin.
"Haka ma babu wani katamammen kudiri da wakilin ya gabatar a majalisar. A takaice, al'ummomin Gusau da Tsafe ba su san dadin wakilcin wannan wakili nasu ba."
Ya kara da cewa: "Za mu hada hannu da kungiyoyin sa-kai na matasa domin mu yi duk mai yiyuwa don ganin mun jawo hankalin wakilin. Idan kuma bai juyo kan yi wa talakawan wannan yanki ayyukan more rayuwa ba, to zamu iya daukar matakin yi masa kiranye kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
©Zuma Times Hausa.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment