This blog was created by Comrade Jibril Almustapha Gusau. The blog will provide you with sound, authentic and genuine news across the world
Friday, 7 July 2017
Matasan Zamfara Ta Tsakiya Ta Aminta Da Sanata Marafa A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jiha...
Kungiyar Hadakar Matasan Zamfara Ta Tsakiya ta bayyana goyon bayanta ga tsayawa takarar neman kujerar gwamnan jihar Zamfara da Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya yake kudurin yi a babban zaben gama gari na shekarar 2019 mai zuwa.
Shugaban kungiyar, Rufa'i Bala UB ne ya bayyana hakan a lokacin wata ziyarar ban-girma ta barka da sallah da kungiyar ta kai wa Sanata Kabiru Garba Marafa a gidan sa dake garin 'Yandoton Daji dake karamar hukumar mulki ta Tsafe.
Bala UB ya bayyana cewa: "Duba da kulawar da Sanatan yake ba al'ummar yankin sa, kungiyarsa ta aminta da cewa, Sanata Kabiru Garba Marafa ne dan takarar da yafi kowa cancantar ya nemi kujerar gwamnan jihar a babban zabe mai zuwa."
Da yake mayar da jawabi a lokacin ziyarar, Sanata Kabiru Garba Marafa yayi wa Kungiyar Hadakar Matasan Zamfara Ta Tsakiya alkawarin babur mai kafa uku (Keke-Napep) har guda Arba'in da Shida (46) da kuma yiwa kungiyar alkawarin samar mata da ofisodhin gudanarwa a dukkan gundumomi Arba'in da uku dake yankin.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment