Friday, 3 November 2017

Shugaba Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2018


Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya tsab domin gabatar da kudurin kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2018.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun Mataimaki na musamman a ofishin shugaban kasa akan kafafen yada labarai na zamani, Malam Bashir Ahmad.

Sanarwar ta nuna cewa, a ranar Talata 7 ga watan Nuwamba na wannan shekara ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2018 a gaban majalisun tarayya.

Sai dai sanarwar bata yi karin haske ba akan abubuwan da kasafin kudin ya kunsa ba.

Rahotanni sun nuna cewa, tuni dai Shugaban ya aike da takarda a Majalisun tarayya domin neman su amince masa ya bayyana a gaban su domin yin bayanai game kasafin kudin.