Saturday, 4 November 2017

PDP Ce Zata Lashe Zaben 2019 a Jihar Zamfara- Ubaidullah Yahaya Kaura



Daga Zuma Times Hausa

Shugaban kungiyar masu hulda da shafukan sadarwa na yanar gizo, wato New Media karkashin Jam'iyyar PDP a jihar Zamfara, Kwamared Ubaidullah Yahya Kaura yace babu ko shakka jam'iyyar PDP ce za ta lashe dukkanin zabukan da za a gudanar a kakar zabe mai zuwa.

Shugaban ya fadi haka ne a wani martani da yake mayar wa mataimakin gwamnan jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala wanda ya ce jam'iyyar PDP ta mutu a jihar Zamfara kuma ba za ta sake dawowa ba.

Mataimakin Gwamnan ya fadi haka ne a gurin bukin ba da katin zama halattaccen zama dan jam'iyyar APC ga tsohon Gwamnan jihar Mahmud Aliyu Shinkafi wanda ya sauya sheka a kwanakin baya.

A martanin da shugaban PDP New Media ya mayar ya ce, kamata ya yi mataimakin gwamnan ya mayar da hankali gurin cigaban jihar kasancewar gwamnatinsu ta APC sun kashe jihar baki daya.

Ya ce, "idan aka duba halin da jihar ke ciki kowa ya san tana cikin mawuyacin hali. Idan ka duba bangaren ilimi, tsaro, ruwan sha, harkar noma, kiwon lafiya, ma'aikata, da kuma walwala da jin dadin jama'a, amma sun kasa tabuka komai a jihar."

Ubaidullah ya ce, in sha Allah jam'iyyar su ta PDP ita ce za ta ceto al'ummar jihar daga wannan mawuyacin halin da jam'iyyar APC ta saka su a ciki.

©Zuma Times Hausa