This blog was created by Comrade Jibril Almustapha Gusau. The blog will provide you with sound, authentic and genuine news across the world
Friday, 21 July 2017
Kungiyar Matasan Hausa/Fulani Za Ta Tallafawa Yaran Karkara Dubu 2 Da Kayan Karatu
Daga Abdulhamid Yaron Malam
A kokarin da take yi na taimakawa wajen habaka sha'anin ilimi a jihar Zamfara, kungiyar matasan Hausa/Fulani ta HAFYDOF ta kai tallafin kayan karatu a wata rugar Fulani ta Tudun Dan Sarki, da kuma kauyen Furfuri dake karamar hukumar mulki ta Bungudu dake jihar Zamfara.
Mai magana da yawun bakin kungiyar, Kwamared Jibril Al-Mustapha Gusau ya bayyanawa wakilin Zuma Times Hausa cewa, "Mun kawo tallafin kayan rubutu ne ga daukacin daliban wannan makaranta dake cikin wannan karkara. Domin mu bayar da tamu gudunmawa wajen habaka ilimi a fadin jihar nan, inda muka tallafa wa yara 300 da kayan karatu. Haka kuma, mun karantar da yaran wasu darussa kamar Turanci, da Lissafi da kuma Hausa. Sannan mun tattauna da shugabannin wannan yanki, mun fahimci irin damuwar da suke da ita akan ilimi. Kuma in Allah ya yarda za mu cigaba da ziyarar yankunan karkara dake fadin jihar nan lokaci zuwa lokaci domin kai tallafi ga makarantun 'ya 'yan talakawa".
Kwamred Jibril ya kara da cewa, "Ina kira ga kungiyoyin sa kai na matasa dake fadin jihar nan ta Zamfara da su mayar da hankali wajen taimakawa yara masu tasowa domin su taimaka wajen habaka sha'anin ilimi".
Kimanin yara 2,000 ne dai kungiyar ta Hausa/Fulani reshen jihar Zamfara take sa ran za su amfana da wannan shiri na bunkasa ilimi a cikin shekarar nan da muke ciki.
©Zuma Times Hausa
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment