Thursday, 22 June 2017

KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA KAI TALLAFI A MASALLATAI


Daga: Comrade-Jibreel Almustapha Gusau

A cigaba da ayyukan taimakon al'ummah a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Kungiyar Muryar Talaka ta kasa reshen Jihar Zamfara ta bayar da tallafin butocin Alwala kimanin guda Dari da Hamsin (150) ga masallatan dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Da yake jawabin yayi gabatar da tallafin, Shugaban Kungiyar Comrade Hafizu Balarabe Gusau ya bayyana cewa: "Kungiyar Muryar talaka ta bayar da waddannan kaya ne domin bayar da gudunmawarta ga addinin musulunci a cikin wannan wata na Ramadan."

Masallatan da suka amfana da wadannan butoci sun hada, Babban masallacin  juma'ah na Tudun Wada, Masallacin Malam Mustapha Ibrahim Sahihi, Masallacin Unguwar Abarma da kuma Babbar Zawuyyar Shehu Balarabe duk a cikin garin Gusau.

No comments: